bayyinaat

Published time: 06 ,April ,2018      10:52:49
Ijtihadi da Takalidi
Hukunc-hukunce su ne: Dokokin da Suka Gangaro daga Mai Shar'antawa don Tsara Rayuwan Dan Adam. Kuma Wadannan Hukunce Hukuncen su ne Suke Iyakance Aikin da ya Hau kan Mutum Wanda zai yi da Wanda zai Bari, kuma sun kasu ne kashi Biyar: 1-Wajibi. 2-Haram. 3-Mustahabi. 4-Makaruhi. 5-Mubahi.
Lambar Labari: 94
Zababbun Hukunce-hukunce

SHIMFIDA:

Hukunc-hukunce su ne: Dokokin da Suka Gangaro daga Mai Shar'antawa don Tsara Rayuwan Dan Adam.
Kuma Wadannan Hukunce Hukuncen su ne Suke Iyakance Aikin da ya Hau kan Mutum Wanda zai yi da Wanda zai Bari, kuma sun kasu ne kashi Biyar:
1-Wajibi.
2-Haram.
3-Mustahabi.
4-Makaruhi.
5-Mubahi.

Wajibi shine: Aikin da a cikin yinsa akwai Maslaha Mai Girma Matuka, Wanda ba'a yi Rangome a kan barinsa ba, don haka dole ne a aikata, kuma Rashin Aikatawan yana sa mutum ya cancanci Azaba, kamar irin su Wajabcin yin Salla da Azumi. 
Haram shine: Aikin da a cikin Aikata shi akwai Fasadi Mai Girma Matuka, Wanda ba'a yi Rangwame akan Aikata shi ba, don haka Wajibi ne a nisance shi, don aikata shi na sa Mutum ya cancanci Azaba, kamar: Haramcin yin Zina da shan Giya.
Mustahabi shine: Abinda a cikin yinsa akwai Maslahan da baikai a tilasta ba, don haka ya halasta a Aikata ko a bari, Amma ana samun lada a cikin Aikatawa, kuma ba'a samun zunubi na barin Aikatawa, kamar: yin Sadaka ga Fakirai da yin Gaisuwa na sallama.
Makaruhi shine: Aikinda acikin yinsa akwai kyama da Fasdi Wanda bai kai ga Haramci ba, ya halasta a Aikata kamar yadda ya halasta a bari, amma akwai lada cikin bari kuma ba laifi cikin Aikatawa, kamar: cin Abinci mai zafi sosai ko yin Barci a Masallaci.
Mubahi shine: Abinda Maslaha da Mafsadansa suka yi daidai, kuma Mukallafi yana da daman zabi na Aikatawa ko rashin Aikatawa, saboda ba lada ko zunubi na Aikatawa ko rashin Aikatawa, kamar: yin Tafiya ko zama.
Mulahaza: Wadannan kashe-kashe na hukunce hukuncen sun shafi Takalifi ne kawai, Acikin hukunce-hukunce Akwai Wad'i, su kuma basu Danfaru da Aikin Mukallafi ba kai Tsaye a Same ko a Rashe, kamar: Inganci da Baci da Sashi da Hani.

IJTIHADI DA TAKALIDI
Yin Aiki da Hukunce Hukuncen Adddini kodai ya zamo akan Ijtihadi, ko akan Taklidi, ko akan Ih'tiyaadi.
Ijtihadi shi ne: Yin kokari Wajen Tsamo Hukunce Hukuncen Shari'a daga Tushensu - kuma mafi Muhimmancinsu su ne:
Al'kur'ani Mai Girma, *Sunna wacce itace:  -Zancen Ma'asumi da -Aikinsa da  -Tabbatarwansa- Bayan Mutum ya karanci ilmukan da zasu Taimake shi akan hakan.  Kuma ana kiran mai iko akan Tsamo Hukunce Hukunce daga wurinda suka Gangaro da [Mujtahidi]. 
Takalidi shi ne: yin Aiki daidai da Ra'ayin Mujtahidi Ayyananne, wato Mukallafi yayi Aiki na (Ibada ko Muaamala) daidai da Fatawar Mujtahidin da ya Cika Sharudda.
Ih'tiyadi shine: kiyaye Dukkan Abinda ke Ganin shi ne Daidai (Ih'timalolin) na Fikihu akan wani Al'amari ta yadda Mutum zai samu Yakini Aikata Abinda aka Dora masa.
Mas'alata :1 Mukallafi shine: Mutumin da ya Balaga, Mai Hankali, Mai Ikon Aikata Abinda aka Dora Masa, kuma Mutum yana Balaga ne ta Hanyar Faruwan Abu uku:
*Yin Mafarki.
*Tsirar gashi mai Gautsi a sama Al'aura.
*Cika shekaru 15 na Kamariyya, ga da Namiji, da kuma cika shekaru 9 na Kamariyya ga 'ya Mace, bisa ga Shahararren zance.
Mas'alata :2 Ana kiran Mujtahidin da wasu suka Masa Taklidi a Hukunce Hukuncensu da [Marjau't Taklid] shi kuma Wanda yabi Mujtahidin ana kiransa da [Mukallidi].
Mas'alata :3 Duk wanda bai kai Matsayin Ijtihadi ba, wato baya da ikon Tsamo Hukunce Hukuncen shari'a daga Tushensu, to ya wajaba a Kansa yayi Taklidi ga Mujtahidin da ya cika ya cika  Sharudda, ko yayi Ih'tiyadi a Matsayin Aiki.
Mas'alata :4 Aikin da ya Doru a kan Mafiyawan Mutane shi ne: yin Taklidi a Ayyukansu, saboda kaiwa ga Matsayin Ihtihadi don tsamo hukunce hukunce Abu ne da bai da sauki sai dai ga 'Yan kadan daga cikin mutane, kuma kamar yadda yin aiki da ihtiyadi bisa ga la'akari da tsayuwansa akan sanin wuraren da ake yi, da yanayin da ake yi, babu masu sanin hakan sai kebantattun mutane, kari akan haka lallai aiki da ihtiyadi yana bukatuwa da Bata lokaci mai yawa.
Mas'alata :5 Ya wajaba akan Marja'i Kari akan ijtihadi da ya cika Wadannan Sharuddan:
*Ya kasance yana raye bisa ga ihtiyadi.
*Balaga.
*Mazantaka.
*Tsarkin Haihuwa.
Kuma bisa ga ihtiyadi wajibi ya kasanc
Mmsaid, [08.01.18 17:57]
e A'alam (Mafi ilimi) Idan ya kasance Fatawowin Fukahaa'u sun Sassaba a Mas'aloli Mabanbanta, kuma an Shardanta Adala gare shi, kai bisa ga ihtiyadi Wujubi ma dole ya kasance ya fi karfin zuciyarsa Mai Dagawa, kuma kada ya kasance mai kwadayin Duniya.
Mas'alata : 6 Wanda yayi Takalidi wani Marja'i sai ya Mutu, ya halasta a gare shi ya cigaba da yi masa Takalidi a sake, akan mas'alolin da yayi Aiki da sune ko a ba akan Mas'alolin da ya yi Aiki da su ba.
Mas'ata :7 A'alam shi ne Wanda ya fi iya tsamo Hukunce-Hukunce a cikin Tushensu a Tsakanin Mujtahidai.
Mas'alata 8: Ana sanin Mujtahidi ne ta Daya daga cikin Hanyoyin nan uku:
1)-Mutum ya Samu Yakini da Kansa, kamar idan ya kasance daga cikin masana, kuma ya kasance yana da iko akan sanin Mujtahidi da A'alam, ta hanyar yi masa Jarrabawa da abinda yayi kama da haka.
2)-Shaidar Adilai biyu daga Ma'abota sani Masu iko akan sanin Mujtahidi da A'alam.
3)-Yaduwa mai Amfanar da ilimi, ko samun Nitsuwa da ijtihadinsa ko A'alamiyyarsa.
Mas'alata 9: Hanyar da ake sanin Fatawar Mujthidi sune:
(1- Ji daga Mujtahidin shi kansa.
(2- Ji daga mutane biyu Adilai.
(3- Ji daga Adili Daya ko da Nakaltowan Sika Wanda za'a samu Nitsuwa da Maganarsa.
(4- koma zuwa ga Risala Amaliyya ga Mukallidinsa idan aka Nitsu da Ingancin Risalar.
Mas'alata 10: Idan Marja'i ya canja ra'ayinsa akan wata Mas'ala, Ya wajaba ga mai Takalidi da shi yin Aiki da Sabuwar fatawa, bai halasta yayi Aiki Tsohuwar Fatawar ba.
Mas'alata 11: Ya wajaba akan Mukallafi Yasan Ma'alolin Shari'a, Wadan da Yau da Gobe yake Jarabtuwa da su, kamar wasu Ma'alolin Salla da Azumi da Tsarki, da wasu daga Mu'amaloli (Gogayya) da Sauransu, Idan rashin Neman sanin ta kai Mutum ga Barin Aikata wajibi ko ta kai shi ga Aikata haram to shi Mai sabo ne.

Wassalam.

Tahir Umar Sulaiman

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: