bayyinaat

Published time: 06 ,March ,2017      09:29:10
Na yi imani da Allah daya ba shi da abokin tarayya, na kuma kafirce wa duk wani abin bauta ba shi ba. Sannan ya ce: Allah (s.w.t) ya aiko ni zuwa ga mutane gaba daya Mai albishir da gargadi ga mutane, sannan zai mayar da kaidin duk mai kaidi kansa.
Lambar Labari: 73
Tsakanin Annabi da Wasu Addinai
Imam Sadik (a.s) ya ce: "Daga Babana Albakir (a.s) daga Kakana Ali Dan Al-Husain (a.s) daga Babansa Husain Shugaban Shahidai (a.s) daga Babansa Ali Dan Abi Dalib (a.s) cewa, wata rana ma’abota Addinai biyar suka hadu a wajan Manzon Allah (s.a.w); Yahudawa da Kiristoci da Dahariyya da Sanawiyya da Mushrikan larabawa.
 Sai Yahudawa suka ce: Ya Muhammad! Mu muna cewa: Uzairu (a.s) dan Allah ne, mun zo mu ga me kake cewa, idan ka bi mu to mun riga ka shiryuwa zuwa ga gaskiya, amma idan ka saba mana zamu yi jayayya da kai. Kiristoci suka ce: Mu muna cewa Isa (a.s) dan Allah ne da ya shiga cikinsa ya hade da shi idan ka bi mu mun riga ka zuwa ga gaskiya amma idan ka saba to ma ja da kai . Dahariyya suka ce: Ya Muhammad! mu muna cewa: Halittu ba su da farko ba su da karshe suna nan har abada, kuma mun zo mu ga me kake cewa, idan ka bi mu mun riga ka fahimtar gaskiya idan kuma ka saba mana to ma ja da kai. Sanawiyya suka ce: Ya Muhammad! mu muna cewa haske da duhu su ne masu juya dukkan al’amura, mun zo mu ga me kake cewa, idan ka bi mu to mun riga ka fahimtar gaskiya amma idan ka saba mana ma ja da kai. Mushrikan larabawa suka ce: Ya Muhammad! Mu muna cewa: Gumaka Ubangizai ne, mun zo mu ga me kake cewa, idan ka bi mu mu mun fika mun riga ka zuwa ga gaskiya da shiriya amma idan ka saba mana to ma ja da kai.
Sai Manzon Allah (s.a.w) ya ce: Na yi imani da Allah daya ba shi da abokin tarayya, na kuma kafirce wa duk wani abin bauta ba shi ba. Sannan ya ce: Allah (s.w.t) ya aiko ni zuwa ga mutane gaba daya Mai albishir da gargadi ga mutane, sannan zai mayar da kaidin duk mai kaidi kansa.
 
Yahudawa
 Sannan ya ce da Yahudawa: Shin kun taru ne nan domin in karbi maganarku babu wata hujja sai suka ce: A’a,. Ya ce: Me ya kai ku ga cewa Uzairu (a.s) dan Allah ne? Sai suka ce: Domin ya raya wa Bani Isra’ila Attaura kuma ba wanda Allah zai yi masa haka sai dansa. Sai Manzon Allah ya ce: Domin me Uzairu (a.s) zai zama dan Allah ga Musa (a.s) alhalin shi ne ya zo wa Bani Isra’ila da Attaura kuma aka ga mu’ujizozi daga gare shi kamar yadda kuka sani. Idan kuwa Uzairu (a.s) zai zama dan Allah saboda karamar raya Attaura, me ya sa kuka kira shi dan Allah ba Musa ba? Sai suka ce: Saboda ya raya wa Bani Isra’ila Attaura bayan ta bace, kuma ba yadda zai ba wani damar haka sai wanda yake dansa. Sai Manzo (s.a.w) ya ce: Ya ya Uzairu (a.s) ya zama dan Allah ba Musa (a.s) ba wanda shi ne ya zo da Attaura din aka ga mu’ujizozi a hannunsa kamar yadda kuka sani? Idan kuwa Uzairu (a.s) zai samu wannan matsayi saboda ya raya Attaura to Musa (a.s) shi ne ya fi cancanta da ya zama dan ba shi ba, domin shi ne ya zo da Attaurar tun farko.
 Idan kuma shi Uzairu (a.s) ya cancanci girmama wa a matsayin da saboda ya raya Attaura to Musa ya cancanci matsayin da ya fi na da, domin ku idan kuna nufi da da ma’anar da kuke gani a Duniya na ‘ya’ya da iyaye suke haifarsu ta hanyar takinsu (kwanciya) daga iyaye maza ga su matan to kun kafircewa Allah kun kwatanta shi da bayinsa kuma kun wajabta masa abin da yake da siffa na fararru, saboda haka ya wajaba ke nan ya zama Fararre abin halitta a wajanku ya zama yana da mahalicci da ya fare shi.
Sai suka ce: Ba haka muke nufi ba, hakika wannan kafirci ne kamar yadda ka fada sai dai mu muna nufin girmamawa kamar yadda wasu malamai sukan kira wanda suke son girmamawa da wani matsayi da "Ya dana!” ko kuma ya ce: "Wannan dana ne” ba domin ya haife shi ba, domin saudayawa yakan gaya wa wanda ba su da wata nasaba da shi hakan. Haka nan yayin da Allah ya yi wa Uzairu (a.s) wannan ni’ima sai muka fahimci cewa bai yi masa haka ba sai don ya rike shi dansa ta hanyar girmamawa ba domin ya haife shi ba. Sai Manzon Allah (s.a.w) ya ce: Wannan shi ne abin da nake gaya muku cewa, idan da wannan Uzairu (a.s) ya zama dansa to wannan matsayi ya fi cancanta ga Musa (a.s) kuma Allah zai kunyata duk mai karya da furucinsa da kansa kuma aniyarsa zata dawo kansa. Ku sani cewa abin da kuka kafa dalili da shi zai lizimta muku fiye da abin da ya wuce haka, domin ku (a misali) kuna cewa: Wani mai girma daga cikinku yakan gaya wa waninsa da ba su da nasaba: "Ya dana!" ba don ya haife shi ba, sai don girmamawa, kuma zaku iya samun wannan mai girma din yana gaya wa wani cewa: "Dan’uwana ne" ya kira wani kuma da "Wannan shehina ne" ko "Babana ne" ko "Shugabana ne" ko "Ya shugabana!" ta hanyar girmamawa, wato duk sa’adda aka samu wanda ya fi girma to sai ya dada masa kalma ta girmamawa fiye da dayan, idan kuwa haka ne a bisa abin da kuke cewa ya halatta Musa (a.s) ya zama Dan’uwan Allah ko Shehinsa ko Babansa ko Shugabansa, domin ya fi Uzairu (a.s) daraja, kamar yadda idan wani ya fi da daraja sai a ba shi girmamawa fiye da shi, sai ya ce masa: "Ya Shugabana! Ko Ya Shehina! Da Ya Ammina! Da Ya Shugabana! ta hanyar girmamawa domin karin girma, shin ya halatta a ganinku Musa (a.s) ya zama Dan’uwan Allah ko Shehinsa ko Amminsa ko Shugabansa ta hanyar girmamawa domin girmansa ya fi na Uzairu (a.s) kamar yadda ake dada girma ga wanda ya fi da a fadarku  a ce da shi: "Ya Shugabana! Ya Shehina! Ya Ammina! Ya Sarkina".

Imam Sadik (a.s) Ya ce: Sai mutanen suka dimauce suka ce "Ya Muhammad! Ka saurara mana mu yi tunani tukuna game da abin da ka ce. Sai Manzo (s.a.w) ya ce: Ku yi duba da zukata masu kudurce yin adalci, Allah ya shiryar da ku.


Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: